✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu mutum na farko da ya kamu da Coronavirus a Kano

An samu mutum na farko da ya kamu da Coronavirus a jihar Kano ranar Asabar. Wata majiya ta nuna cewa mutumin da ya kamun wani…

An samu mutum na farko da ya kamu da Coronavirus a jihar Kano ranar Asabar.

Wata majiya ta nuna cewa mutumin da ya kamun wani babban  mutum ne da ya koma Kano  daga Legas.

Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Aminu Tsanyawa ya ba da tabbacin faruwar lamarin, sai dai ya ki yin karin haske  game da mutumin da ya kamu.

Ana sa ran gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai yi wa jama’ar jihar bayani game da lamarin nan ba da jimawa ba.