Da Dumi Dumi

An samu mutuwa ta farko a Najeriya sakamakon Coronavirus

A karo na farko an samu wanda ya mutu sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus a Najeriya.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta tabbatar da mutuwar a shafinta na Twitter cewa wanda ya rasu wani mutum ne mai shekara 67 da ya dawo daga jinya a Birtaniya.

Hukumar ta ce da ma dai marigayin yana fama da cutar sukari wato diabetes, kuma jinya ce ta kai shi Birtaniya.

Tuni dai rahotanni suka ambato iyalan mutumin, Sulaiman Achimugu, wanda tsohon manajin darakta ne a Hukumar Kayyade Farashin Man Fetur (PPMC), suka fitar da wata sanarwa suna bayyana cewa ya rasu ne kwanaki kadan bayan ya killace kansa.

Sanarwar mai dauke da sa-hannun Abubakar Achimugu ta kuma ce “da kanshi ya kira NCDC bayan da ya fara jin alamun COVID-19, aka kuma dauake shi zuwa Asibitin Koyarwa, inda ya rasu yayin da akae jinyarsa”.

ADVERTISEMENT

Zuwa yanzu dai adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya ya kai 36.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya