Daily Trust Aminiya - An samu Radamel Falcao da laifin yin zuke a shekarunsa
Subscribe

An samu Radamel Falcao da laifin yin zuke a shekarunsa

Rahotannin da wasu kafofin watsa labarai suka baza a shekaranjiya Laraba ya tabbatar an samu sabani a shekarun da shahararren dan kwallon Atletico Madrid da ke Sifen da ya canza sheka zuwa kulob din PSG da ke Faransa a kan Yuro Miliyan 60 ya gabatar wa hukumar FIFA.
Rahoton ya ce Hukumar FIFA ta tabbatar dan kwallon yana da shekara 29 ne kamar yadda ya bayyana a taskar ajiyarta maimakon shekara 27 da dan kwallon yake ikirari a halin yanzu.
Kafar sadarwar Youtube ce ta bi diddigin rayuwar dan kwallon inda ta kalato yana amfani ne da ranar 10 ga watan Fabrairun 1986 a Hukumar FIFA a matsayin ranar da aka haife shi alhali kuma bayanan da aka samo daga makarantar firamaren da ya halarta sun nuna an haife shi ne a ranar 10 ga watan Fabrairun, 1984.
Haka kuma dan kwallon ya nuna an haife shi ne a babban birnin Kolombiya watau Bogota maimakon bayanin da aka samu a makarantar firamaren da ya halarta cewa an haife shi ne a garin Santa Marta da ke Kolombiya.
Wadannan bayanai da dan kwallon ya gabatar ne suka tayar da hankalin Hukumar da kuma masu ruwa da tsaki a harkar kwallo.
Sai dai a tattaunawar da wasu kafofin yada labarai suka yi da mahaifin Falcao mai suna Radamel Garcia Senior ya bayyana cewa an haifi dan nasa ne a garin Santa Marta a shekarar 1986.
Mahaifin ya kara da cewa akwai yiwuwar Hukumar FIFA ta yi kuskure a wajen shigar da bayanan dan nasa a taskarta kuma ya yi fatan hukumar za ta gyara wannan kuskure cikin gaggawa.
Ana sa ran Hukumar za ta gudanar da bincike a kan al’amarin, muddin aka samu dan kwallon da laifi akwai yiwuwar ya fuskanci hukunci.
Sannan dan kwallon zai fuskanci barazanar rasa kima a idon duniya idan  aka tabbatar ya yi magudi.

texem
More Stories