✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu saukin ta’addanci a Zamfara – Walin Sakajiki

An bayyana cewa an samu saukin ta’addanci a Jihar Zamfara sakamakon sulhu da Gwamnan Jihar ya yi da ’yan ta’addan a jihar. Alhaji Suleiman Yunusa…

An bayyana cewa an samu saukin ta’addanci a Jihar Zamfara sakamakon sulhu da Gwamnan Jihar ya yi da ’yan ta’addan a jihar.

Alhaji Suleiman Yunusa Walin Sakajiki a Karamar Hukumar Kauran Namoda ne ya bayyana a haka a zantawarsa da Aminiya a Kaduna.

Ya ce ko shakka babu an samu saukin kai hare-hare duk da cewa akwai wasu yankuna da barayin ke lebe cikin daji da tsaunuka.

“Sulhu da Mai girma Gwamna ya yi da wadannan mutane an samu sauki kwarai da gaske. Sai dai akwai wasu garuruwa da ke cikin daji inda barayin ke zama kamar Badaku da Dagarwa da Abaniyawa da Kabaje da Zankuwa. Kowane gari za ka yi tafiya a cikin daji na tsawon kilomita 20 kuma daga Sakajiki za ka iya bullawa har zuwa Maradun. Kuma barayin nan na boye a cikin daji da tsaunuka wanda hakan ya sa yake da wuya ka gane su,” inji shi.

Ya ce, “Amma a yanzu matakan da ake dauka sun yi kyau don haka mu za mu rika bincike idan mun ga bako domin sanin daga inda yake.”

Ya ce mutanen Sakajiki mutane ne masu ilimin boko da na addini kuma ’yan kasuwa ne fitattu domin sun rike mukamai har a jihohin Legas da Kaduna a fannin kasuwanci.

Basaraken ya ce yawancin batagari da aka kama a garin Sakajiki ’yan kwanakin nan baki ne ba ’yan asalin garin ba ne.

“Wannan ke nuna mutanen Sakajiki ba cima-zaune ba ne, kuma masu neman abin hannunsu ne sannan masu neman ilimi ne ta kowane fanni.  Wadanda aka kama baki, ne ba ’yan asalin Sakajiki ba ne, kuma an kama su ne da hadin kan ’yan asalin Sakajiki. A yanzu haka akwai wadansu barayi da suka zo suka ce wai suna bin wadancan barayi da aka kama kudi, don haka jama’ar Sakajiki ne za su biya kudin ko su kai musu hari.”

“Don haka muke kira ga Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle, ya kalli wannan al’amari da idon rahama domin kuwa mun ji dadin zuwansa da zamansa Gwamna ya dauki matakin kare garin namu,” inji shi.