Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An samu sauyi na kwarai a Zamfara

Bayan gaisuwa, ina so in isar da sakon taya murna ga mutanen Jihar Zamfara bisa fara samun zaman lafiya a jihar. Sannan ina fata wannan sulhu da ake yi zai dore, kuma za a samu dawwamammen zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.

Cikin kankanen lokaci bayan da Gwamnan Jihar Alhaji Bello Matawalle ya hau karagar mulki, Zamfarawa sun fara ganin sauyi da aiki da cikawa musamman a bangaren tsaro.

ADVERTISEMENT

Jihar Zamfara ta dade tana fama da matsananci rashin tsaro, musamman rikice-rikicen barayin shanu da ’yan bindiga. Hakan ya sa matasan jihar da dama suka rika yin zanga-zanga a lokuta da dama a garuruwa daban-daban. A lokacin duk wata ribar dimokuradiyya ba shi ne lissafinsu ba, babban ribar da suke nema wajen ’yan siyasa ita ce kawai a samu zama lafiya mai dorewa.

Allah Ya kawo Bello Matawalle, wanda wadansu mutane suke tunanin ba zai iya ba. Amma cikin ikon Allah da iyawarSa, sai ga shi Bello Matawalle ya dauki hanyar shawo kan lamarin.

ADVERTISEMENT

Tuni ya jagoranci jami’an tsaro suka shiga cikin daji suka gane wa idonsu abin da ake ciki. Sannan ya zauna da bangarorin da abin ya shafa. Kuma yanzu haka an zauna da dukkan bangarorin domin yafiya da sulhu, kuma duk sun amince. Kuma abin mamaki shi ne yadda ’yan bindigar suka amsa kira, har da wadansu shugabannin ’yan bindigar da ake tunanin ba za su halarci taron ba musamman a Birnin Magaji duk sun halarci taron kuma sun amince su yafe wa juna su zauna lafiya.

A wajen taron sulhun, ’yan sa-kai sun amince Fulani su ci gaba da harkokinsu a kasuwanni, su kuma suka amince manoma su shiga daji su ci gaba da harkokin nomansu, inda a nan take wani yake cewa ko yanzu idan akwai wanda zai je ya tashi ya tafi.

Wannan ba karamin abin murna ba ne, kuma da yardar Allah nesa ta zo kusa. Domin bayan harkokin samar da zaman lafiya, Gwamna Bello Matawalle ya fara kokarin samar da ayyukan yi wanda tun farko rashin aikin yi yana taimakawa wajen kara rura wutar rikicin. Dama kuma idan har ana so a magance matsalar rashin tsaro, to dole sai an samar wa matasa ayyukan yi domin rage zaman banza. Tuni kamfanin takin zamani na jihar ya fara aiki, inda zai samar wa matasa aiki, sannan Zamfarawa su samu takin da za su koma noma.

A karshe ina kira ga Gwamna da sarakuna da sauran wadanda abin da ya shafa su rike alkawari su tabbatar wannan sulhu ya tabbata domin samun tabbataccen zaman lafiya a Zamfara.

Mu kuma al’umma mu ci gaba da addu’a. Da fatan Allah Ya tabbatar mana da alheri.

 

Mubarak Dangarba. 08022582833