Da Dumi Dumi

An samu tarin kyankyasai masu rayuwa a cikin kunnen mutum

Likitoci sun gano tarin wasu kyankyasai da suke rayuwa a cikin kunnen wani mutum da ke fama da ciwon kunne a kasar China.

Marar lafiyar mai suna Mista Lu, ya ziyarci asibitin gundumar Guangdong da ke Kudu maso Gabas na kasar China a watan Oktoban da ya gabata. Jaridar New York Post ta wallafa rahoton AsiaWire cewa, Mista Lu ya bayyana wa likitocin cewa, ya dade yana jin zafi a cikin kunnensa na hannun dama.

Wani kwararre likitan kunne da hanci da makogoro Asibitin Sanhe mai suna Dokta Zhong Yijin, wanda ya yi wa  marar lafiyar tiyata ya bayyana wa majiyar AsiaWire cewa: “Kunnensa yana yi masa zafi kamar wani abu mai rai yana yawo a cikin kunnen, kuma yana yawan kawo masa rashin kwanciyar hankali.”

Mista Lu, ya ce ’yan uwansa sun taba haska cikin kunnensa suka samu tarin kyankyasai a ciki. Dokta Yijin, ya yi wa Mista Lu gwajin kunnen ya gano kyankyasai iyaye da ’ya’ya da suke rayuwa a cikin kunnen.

Jinsin kyankyasan irin na kasar Jamus ne, kamar yadda Dokta Yijin, ya sanar ya kuma ce akwai sama da ’ya’yan kyankyasai 10 da suke rayuwarsu a cikin kunnen.

ADVERTISEMENT

Mista Lu, ya ce wani lokaci yana samun wani abu kamar abinci a gadonsa da daddare, kamar yadda ya sanar wa kafar labaran yankin.

Dokta Jiang Tengdiang, Mataimakin Shugaban Asibitin, ya ce akwai yiwuwar kyankyasan sun shiga cikin kunnen ne lokacin da suke shirin kyankyasar kwan da suka yi.

Likitocin asibitin sun yi amfani da wani karfen fitar da karamin abu a jikin mutum wajen ciro kyankyasan da ’ya’yansu daga kunnen. Ma’aikatan Asibitin Sanhe sun bayyana wa kafar labarai ta AsiaWire cewa aikin yi wa Mista Lu tiyatar ciro kyankyasan ya dan samu karamin rauni ne kawai a cikin kunnen.

An salami Mista Lu daga asibitin inda zai ci gaba da shan magungunan da za su rage masa radadin ciwon kunnen.

Dokta Tengdiang, ya shawarci wadanda suke fama da irin wannan cuta su kasance masu cin abincin mai inganci tare da kwana cikin gidan sauro sannan su toshe duk wata kofa da kyankyaso zai iya shiga cikin dakinsu.

“Wannan wata hanya ce da za ta hana kwari shiga cikin hanci ko kunne,” inji Tengdiang.

A bara ce wata mata a Jihar Florida ta Amurka ta samu irin wannan larurar. Kamar yadda kafar labarai ta Self.com ta sanar, matar mai suna Katie Holley, ta ce mijinta ya gina sabon gida a jihar saboda sauyin yanayi da ake samu a jihar kyankyasai suka yi yawa a cikin gidan. Bayan wani lokaci wata rana ta tashi daga barci sai ta ce, tana jin wani abu na yawo a cikin kunnenta da aka duba sai ga kyankyaso a cikin kunnen. Da farko ta fara saka auduga da nufin ciro abin da ke cikin kunnen sai kyankyason ya ci gaba da shigewa cikin kunnen.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya