Da Dumi Dumi

An samu tsaikon gurfanar da Wadume gaban shari’a

Hamisu Bala Wadume (a hagu) da Kyaftin Ahmed Tijjani Balarabe (a dama)
Hamisu Bala Wadume (a hagu) da Kyaftin Ahmed Tijjani Balarabe (a dama)

An samu tsaiko wajen gurfanar da Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume tare da wadansu mutum 10 gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, saboda rashin bayyanar wadansu daga cikin wadanda ake zarginsu tare wadanda galibinsu sojoji ne.

Mai shari’a Binta Nyako, gabanin ta dage shari’ar zuwa 30 ga Maris, ta umurci Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya, da lallai ya mika sojojin da ake zarginsu da hannu a shari’ar.

Wadanda ba su halarci zaman kotun ba, sun hada da wadansu sojojin Najeriya ne da ake tuhumarsu da hannu a karar a matsayin – wadanda ake tuhuma  na biyu zuwa na 11.

Cikin mutum 20 da ake zargi, akwai Kyaftin Ahmed Tijjani Balarabe da Sitaf  Saja Dabid Isiah da Saja Ibrahim Mohammed da Kofur Bartholomew Obanye da Kurtu Mohammed Nura da  sauransu.

Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ne yake tuhumar wadanda ake zargin kan laifuffuka 16 da suka hada da ta’addanci da kisan gilla da satar mutane da kuma mallaka ko yawo da makami ba bisa ka’ida ba.

ADVERTISEMENT

Ana zargin Wadume da hannu dumu-dumu a ayyukan sace mutane domin fansa a Jihar Taraba. Sai dai ya tsare daga hannun ’yan sanda a ranar 6 ga Agustan bara; inma aka sake kama shi ranar 19 ga watan a  Kano.

Wadume ya yi bayani dalla-dalla kan yadda ya ce sojoji suka kubutar da shi daga kamen da ’yan sanda suka yi masa da farko; inda aka ya ce sojojin sun kashe wadansu ’yan sandan rundunar yaki da miyagun laifuffuka da a lokacin suke rike da shi kan hanyarsu daga Ibbi zuwa Jalingo a ranar 6 ga watan Agustan bara.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya