✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sanya alama don rushe sakatariyar sabuwar PDP da gidan Kwankwaso a Abuja

Ana wani yunkuri da ake ganin na karya lagon sabuwar Jam’iyyar PDP ne Hukumar Birnin Tarayya ta sanya jan fenti domin rushe ginin Sakatariyar sabuwar…

Gidan Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamnati ke neman rushewa a AbujaAna wani yunkuri da ake ganin na karya lagon sabuwar Jam’iyyar PDP ne Hukumar Birnin Tarayya ta sanya jan fenti domin rushe ginin Sakatariyar sabuwar PDP a karkashin jagorancin Abubakar Baraje da ke da matsuguni a ofishin tuntuba na gwamnatin Jihar Adamawa da ke Gundumar Maitama a Abuja.
Yayin da kuma hukumar birnin ta sanya jan fenti a wani gida na Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da ke Wuse Zone 7 domin rushe shi, bayan ta kulle shi ba shiga ba fita a ranar Talatar da ta gabata.
Hukumar Raya Birnin Tarayya (FCDA), ta rubuta alamar rushe sakateriyar ce da ke Lamba 4, Oyi Riber Crescent tun ranar 11 ga Oktoban bana.
A ranar Juma’ar da ta gabata ce wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa bangaren Kawu Baraje na sabuwar PDP haramtacce ne, kuma ta umarci Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi aiki da Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar PDP a karkashin Bamanga Tukur kadai a mtsayin halattacciyar PDP.
An hakikance sanarwar shirin rushe gidan wani yunkuri ne na shugabannin PDP domin karya lagon sabuwar PDP. Domin kotun na yanke hukunci, sai Sakataren Labarai na Jam’iyyar PDP ta kasa, Olisa Metuh, ya yi gargadin cewa jam’iyyar ba za ta lamunci ayyukan masu ballewar ba.
 “Muna son mu nanat cewa, duk wani rukuninn jama’a da suke bayyana kansu a matsayin shugabannin wanna jam’iyya tamu da suke sojan gona wajibi ne a dauke su a matsayin aikata miyagun ayyuka.”
Ya kara da cewa, “Daga yanzu shugabannin Jam’iyyar PDP ba za su sake amincewa da duk wani taro ko furuci ko takardar sanarwa ko kowane irin aiki a karkashin suna ko tuta ko Gwamna  Murtala Nyako na Jihar Adamawa da takwaransa Injiniya Kwankwaso na Jihar Kano suna cikin gwamnoni bakwai da ke bangaren Baraje.