✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a Edo

Gwamnatin Edo ta sanya dokar hana fita na sa'a 24 har sai abin da hali ya yi

Gwamnatin Jihar Edo ta sanya dokar hana fita na sa’a 24 a fadin jihar har sai abin da hali ya yi.

Gwamnatin ta sanar da hakan ne bayan ‘yan daba sun yi kaka-gida a zanga-zangar #EndSARS a jihar inda aka gan su dauke da muggan matkamai sun tare babbar hanyar Benin-Agbor-Asaba.

Da yake sanar da haka ta shafinsa an Twitter, Gwamna Godwwin Obaseki ya ce, “Dokar hana fitar za ta fara aiki daga karfe 4 na yammacin yau Litinin 19 ga Oktoba, 2020”.

Sanarwar Obaseki ta bakin Sakataren Gwamnatin Jihar Edo, Osarodion Ogie ya fitar ya ce, “daukar matakin ya sama wajibi saboda abin tashin hankalin da aka ga ‘yan daba masu fakewa da zanga-zangar #EndSARS ke kai farmaki suna kuma fasa shaguna suna satar kayan jama’a da na hukumomi.

Rahotanni sun ce masu zanga-zangar ta #EndSARS a Jihar Edo sun kone ofisoshin ‘yan sanda guda biyu a Karamar Hukumar Ikpoba-Okha.

Gwamantin Jihar ta ce masu zanga-zangar sun kuma kai hari a gidan yarin da ke garin Benin da nufi sakin wasu fursunoni inda aka yi musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro.

Sanarwar ta ce duk da cewa jihar na mutunta ‘yancin jama’a na gudanar da zanga-zanga, ba za ta zura ido tana ganin ‘yan daba sun dauki doka a hannunsu su ba suna cutar da ‘yan kasa da ba su ci ba ba su gani ba.