✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sassari wani matashi a yankin Jama’a

A karshen makon jiya ne mutanen Unguwar Aduan II, da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna suka wayi gari da ganin daya daga cikin…

A karshen makon jiya ne mutanen Unguwar Aduan II, da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna suka wayi gari da ganin daya daga cikin matasan garin mai suna Emmanuel Madakiya kwance cikin jini kusa da rafin Aduan yana neman taimako sakamakon sassare shi da aka yi.

Sunday Emmanuel, daya daga cikin mutanen da aka kira domin kai masa dauki ya shaida wa Aminiya cewa wani mafarauci mai suna Emmanuel Bala da ya yi sammako don duba tarkonsa a cikin daji ne ya yi kicibis da matashin kwance cikin jini yana neman taimako.

Ya ce duk da halin da ya tarar da matashin a ciki na rai kwakwai-mutu-kwakwai amma ya iya kokartawa cikin karfin hali wajen ambaton wani mai suna Emma a matsayin wanda ya yi masa aika-aikar.

Bayan ceto shi ne aka garzaya da shi babban asibitin garin Kafanchan, inda ake ci gaba da kula da lafiyarsa.

Yayin da Aminiya ta leka asibitin ta same shi yana barci. Sai dai wani matashi da Aminiya ta zanta da shi wanda ya nemi a sakaya sunansa ya yi kira ga jami’an tsaro na farin kaya da masu kaki da su tsaurara bincike a kan wannan lamari, domin irin hadarin da hakan zai jefa garin a ciki.

Matashin ya ce da a ce wanda aka sara ya mutu da watakila wadansu su ce Fulani ne suka kashe shi karshe wani abu ya biyo baya.

Lokacin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Hukumar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Sabo Yakubu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce hukumarsu ta yi nasarar kama mutum daya da ake zargi a kokarinta na zakulo wadanda suka yi wannan aika-aikar kuma ta baza jami’anta a kai.