✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sayar da tattabara a kan miliyan N700

Sabon tarihi ya kafu yayin da aka sayar da wata tattabarar tsere a kan Fam miliyan daya da dubu dari shida bayan an yi gwanjonta…

Sabon tarihi ya kafu yayin da aka sayar da wata tattabarar tsere a kan Fam miliyan daya da dubu dari shida bayan an yi gwanjonta a intanet a kasar Belgium ga wani mutumin kasar China.

A cikin rabin sa’ar da ta gabata gabanin samun wanda ya fi sanya kudi, wasu ’yan kasar China biyu masu lakabin Super Duper da Hitman, sun fafata wajen daga farashin tattabarar mai suna New Kim, inda a karshe Super Duper ya samu nasarar mallakarta.

Tattabarar mai shekara biyu da haihuwa, an fara gwanjonta ne a kan Fam 200 a karon farko a ranar 2 ga watan Nuwamba, amma bayan takarar neman sayen ta da makonni biyu, Super Duper ya saye ta a kan Fam miliyan 1.6, kimanin Naira miliyan 700 ke nan a kudin Najeriya.

Super Duper ya mallaki tattabarar ce bayan ya kasance wanda ya mallaki wani namijin tattabaran mai suna Armando wanda kuma ake wa lakabi da ‘Lewis Hamilton’ din tseren tattabaru.

A 2019 ne Super Duper ya mallaki Armando bayan ya saye shi a kan Fam miliyan daya da dubu ashirin da biyar kamar yadda kafar watsa labarai ta MSN ta wallafa.

Kurt Van de Wouwer, wanda shi ne mutumin da iyalansa suka raini wannan New Kim a yankin Berlaar kusa da Antwerp a kasar Belgium, ya ce sun yi mamakin samun wannan labarin darajar da New Kim ta yi a kasuwa kasancewarta mace fiye da Armando wanda namiji ne.

New Kim ta samu lambar yabo ta tattabara mafi karancin shekaru da ta yi gasar tsere karon farko a shekarar 2018.

Tsere mai dogon zango da tattarabaru ke yi a kasar China na kara shahara wanda kuma ya sa farashi da darajar tattabaru ke karuwa a kasar Belgium, cibiyar tseren tsuntsaye.