Da Dumi Dumi

An sayi dan damben gargajiya na farko a Kano

Bisa al’ada ’yan wasan damben gargajiya kan canja sheka daga wani yanki zuwa wani bisa radin kansu ba tare da an ba su ko sisi ba. Sai dai a karo na farko lamarin ya canja, inda aka fara gudanar da cinikin wani dan wasan damben gargajiya daga Arewa mai suna Dan Inyamuri Shagon Shagon Bahagon Balangada zuwa Kudu wato iyalan Dan China kan Naira dubu hudu.

Sakataren Kungiyar Magoya Bayan Wasan Damben Kudawa  Dokta Ibrahim ne ya jagoranci wannan ciniki kuma a take dan wasan ya canja sunansa daga Shagon Shagon Bahagon Balangada zuwa Shagon Shagon Jafaru.

A cewar Dokta Ibrahim duk da cewa akwai hamayya a tsakaninsu da bangaren Arewa, amma hakan ba zai sa su ki daukar dan wasan da ya fito daga yankin ba, musamman  a lokacin da ake kakar wasanni.

Ya yi albishir ga ’yan kallo cewa sabon dan wasan da suka yi cinkinsa zai taka rawar gani a Gasar Dambe ta Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje wanda za a yi bayan Karamar Sallah.

Hakan ya bude wani sabon shafi a harkar wasan damben gargajiya domin hakan ya sa yankin Arewa sun shiga zawarcin dan wasan damben Gurumada   wato Shagon Bahagon Mai Bulala.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya