✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An shawarci Elneny ya gaggauta barin kulob din Arsenal

An shawarci dan kwallon kulob din Arsenal da ke Ingila Mohammed Elneny ya gaggauta canja sheka zuwa wani kulob da zarar an bude kasuwar cinikin…

An shawarci dan kwallon kulob din Arsenal da ke Ingila Mohammed Elneny ya gaggauta canja sheka zuwa wani kulob da zarar an bude kasuwar cinikin ’yan kwallo a wannan wata.  Wannan shawara ta fito ne daga bakin tsohon kocin Elneny a Masar Hamdy Nouh.

Nouh ya ce bai ji dadin yadda dan kwallon ya rasa gurbinsa a kulob din na Arsenal ba tun bayan da sabon koci Unai Emery ya karbi ragamar horar da kulob din a kakar wasa ta bana ba.

Elneny wanda ya rika buga wasa a kan kari a karkashin tsohon koci Arsene Wenger, yanzu yakan shafe makonni a benci ba tare da  Emery ya sanya shi a wasa ba,  hakan ya sa tauraruwarsa ta fara dushewa.

A kan haka ne Nouh ya ba shi shawarar ya gaggauta barin Arsenal don ya samu damar farfado da martabarsa.

Elneny dai ya buga wa Arsenal kwallo ne na tsawon mituna 59 kacal tun bayan da aka fara kakar wasa ta bana da hakan ke nuna lallai yana fuskantar matsala.

Wenger ya sayo Elneny ne daga kulob din Basel a kan Fam miliyan 7 a shekarar 2016.