✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An shawarci manoman citta su inganta nomanta

An shawarci manoman citta su daina algushi wajen gyara cittarsu idan suka noma don kara daga darajar cittar da aka yi amanna da ingancinta a…

An shawarci manoman citta su daina algushi wajen gyara cittarsu idan suka noma don kara daga darajar cittar da aka yi amanna da ingancinta a kasuwannin duniya.

Shugaban Kwamitin Amintattu na Kungiyar Manoma Citta ta Kasa (NGAN), Sanata Haruna Azeez ne ya yi wannan kira jim kadan bayan kammala zaben sababbin shugabannin kungiyar da aka gudanar a garin Kafanchan a Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna.

Sanata Azeez ya yi kira ga manoman su tabbatar sun tsabtace cittar ta hanyar cire duwatsu da kasa kafin durawa a buhuna don kara nauyinsu, dabi’ar da ya ce wadansu batagari masu neman kazamar riba na yi, wadda ya ce hakan na daya daga cikin halayen da suka janyo karyewar darajar cittar da ta yi sanadiyyar karyewar manoman.

A  jawabin sabon shugaban kungiyar, Dokta Nyam Leo Yusuf, ya nuna farin cikinsa ga ’ya’yan kungiyar bisa damar da suka ba shi, inda ya yi alkawarin tafiya da kowa cikin wa’adin da zai jagoranci kungiyar.

Dokta Yusuf, ya tunatar da kananan dillalan citta da su rika taimaka wa manoma ta hanyar sanar da su gaskiyar farashin da ake sayarwa gudun kada su rika tashi a huhun ma’ahu.

Ya ce dole ne su ma kananan ’yan kasuwa da kananan dillalan da ake amfani da su wajen sayen citta daga manyan ’yan kasuwa su hada kansu, inda ya yi alkawarin tattara rajistar dukkan kungiyoyin masu harkar citta don tattaunawa da su kan hanyoyin da za su bi don bunkasa harkar.

Sababbin shugabannin da za su gudanar da kungiyar na tsawon shekara hudu sun hada da Dokta Nyam Leo, a matsayin Shugaba, sai Adeniji Akinwumi Moses, Mataimaki da Ikenyirimba Amaechi a matsayin Sakatare, da Kenneth Suwa, a matsayin Sakataren Kudi da kuma Adams Nathaniel mai bada shawara kan Harkokin Shari’a na Kungiyar.