✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An soke biyan kudin makaranta a Abuja

Ministan Birnin Tarayya, Muhammad Musa Bello ya ba da umarnin bude makarantu a ranar Litinin mai 12 ga wannan wata. Shugaban Kwamitin Tsara Bude Makarantu…

Ministan Birnin Tarayya, Muhammad Musa Bello ya ba da umarnin bude makarantu a ranar Litinin mai 12 ga wannan wata.

Shugaban Kwamitin Tsara Bude Makarantu bayan annobar coronavirus da Ministan ya nada, Dokta Fatima Abdurrahman ce ta sanar da hakan a zantawarta da ’yan jarida a Abuja.

Dokta Fatima ta ce ministan ya soke karatu zango na 3 inda ya bukaci makarantu da su yi wa dalibansu bita a kan karatun zango na 2 tare da shirya masu jarabawa a kai, cikin mako 2 bayan bude makarantun.

Ministan ya kuma gargadi makarantu masu zaman kansu da su guji karbar kudin makaranta na zango na ukun da aka soke, tare da tabbatar da cewa dalibai ba su zarce 25 ba a cikin aji komai girmansa.

“Dole ne kuma kowace makaranta ta tanadi dakin ajiye dalibi ko daliba da a ka gano zafin jikinsa ya wuce kima, inda malaman jinya za su kula da shi kafin isowar iyayensa don kai shi inda ya da ce.

“Dole ne kowace makaranta ta magance duk wani abin da zai iya jawo cunkushewar dalibai a waje guda, tare da bin sharudan da a ka gitta.

“Duk makarantar da ta saba ka’idojin har a ka kai ga barkewar annoba, za ta fuskanci hukuncin ladabtarwa ciki har da rufe makarantar”, inji ministan.

Ya ce an dauki matakin bude makarantun ne bayan nazari a kan lamarin tare da tuntubar Kwamitin Shugaban Kasa kan COVID-19, inda aka gano cewa ana iya bude makarantu a Abuja bayan daidaituwan lamurra gwargwadon hali.