✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tabbatar wa Ibrahim Tanko mukamin Babban Jojin Najeriya

A shekaranjiya Laraba ce, Majalisar Dattawa ta tantance tare da tabbatar da Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad mukaminsa na Babban Jojin Najeriya. A yayin da…

A shekaranjiya Laraba ce, Majalisar Dattawa ta tantance tare da tabbatar da Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad mukaminsa na Babban Jojin Najeriya.

A yayin da yake amsa tambayoyi daban-daban daga sanatoci a yayin tantance shi a zauren majalisar, sabon Babban Jojin ya bayyana cewa masu gudanar da bangaren shari’a a kasar nan ’yan Najeriya ne, don haka halayensu ba lallai ne su saba da na al’ummar Najeriya ba. “Na sha fadin cewa Bangaren Shari’a na Najeriya ne, masu tafiyar da shi ma ’yan Najeriya ne, don haka ba na yin mamaki idan an samu wadansu masu shari’a suna aikata rashin gaskiya. Sai dai kuma hakan ba yana nufin cewa ba za a iya ganowa da hukunta irin wadannan bara-gurbin alkalai da suka keta doka ba, ne” inji shi.

Ya ce abin takaicin kuma shi ne, mafi yawan masu aikata rashin gaskiya kamar amsar hanci da rashawa, ana samun su ne a kananan kotuna ba manya ba. Ya ce an fi samun matsalolin rashin gaskiya ne a kotunan yanki da na majistare.

Da yake bayyana kalubalen da ke fuskantar sashin shari’a na kasar nan, ya bayyana cewa lallai akwai bukatar goyon baya da hadin kan bangarorin zartarwa da na majalisun kasa, domin magance irin wadannan matsaloli da kalubale. Ya ce nan gaba zai yi kokarin gabatar da sababbin tsare-tsare kan yadda za a gyara wasu daga cikin dokokin kasar nan ga majalisun tarayya.

Kafin tabbatar da shi a matsayin cikakken Babban Jojin Najeriya, Ibrahim Tanko yana kan mukamin ne a matsayin riko tun daga ranar 25 ga Janairun bana, lokacin da aka dakatar da tsohon Babban Jojin Najeriya, Mai shari’a Walter Onnoghen saboda zarginsa da kin bayyana kadarorinsa kamar yadda doka ta tanada.