✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tafka kurakurai a zabukan baya -INEC da CDD

kungiyar Samar da ci Gaban Harkokin Dimokuradiyya a Najeriya (CDD) mai samun tallafin kungiyar OSIWA da hadin guiwar Hukumar Zabe ta Najeriya (INEC) sun nemi…

 Farfesa Attahiru Jega Shugaban Hukumar INECkungiyar Samar da ci Gaban Harkokin Dimokuradiyya a Najeriya (CDD) mai samun tallafin kungiyar OSIWA da hadin guiwar Hukumar Zabe ta Najeriya (INEC) sun nemi shugabannin hukumomin zaben jihohi da gwamnoni su gyara tsarin gudanar da zabukan kananan hukumomi don a samu ingantuwar lamurran zabe a Najeriya.
Kiran ya fito ne a lokacin da kungiyar ta CDD ta shirya taron masu ruwa da tsaki kan harkar gudanar da zabukan kananan hukumomi da kuma yadda hukumomin zaben jihohi ke gudanar da ayyukansu. An nazarci wani littafin da kungiyar ta rubuta sakamakon binciken da ta gudanar a hukumomin zaben jihohin Bauchi da Edo da Imo da Kaduna da Lagos da Pilato game da yadda suka aiwatar da zabukan kananan hukumominsu.
Furofesa dahiru A. Yahaya na Jami’ar Bayero ta Kano, a cikin jawabinsa ya bayyana muhimmancin barin mutane su zabi shugabannin da suke so. Ya nuna illolin da ke tattare da tilasta shugabanni a kan mutane, lamarin da ka iya kawo nakasar mulkin dimokuradiyya da kuma  janyo nakasu ga Shugabannin, ta yadda ba za su iya gudanar da adalci ga wadanda suke jagoranta ba, har a kai ga lalacewar lamurra.
Furofesa dahiru ya kara da cewa, magudin zabe shi ne kashin bayan irin matsalolin da ake fuskanta a kasashen duniya, don haka ya shawarci masu ruwa-da-tsaki kan zabuka su kasance masu tsayar da adalci don a samu gamsuwa da zabukan da ake yi a kasa baki daya.
Farfesa Jibril Ibrahim shi ne shugaban kungiyar CDD, mai samun tallafin OSIWA, cikin jawabinsa ya bayyana muhimmancin inganta zabukan kananan hukumomi saboda shi ne kashin bayan ci gaban harkokin mulkin dimokuradiyya.
Ya ce a dukkan binciken da suka gudanar tare da masana, sun fahimci matukar ba an gyara matsalolin zabe daga tushe ba, zai yi wahala a samu ci gaban ingancin rayuwa.
Dokta Umar Mas’ud na tsangayar nazarin siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano ya ja hankalin hukumar zabe ta Najeriya wajen nuna wa hukumomin zaben jihohi muhimmancin zama a fahimci juna da jam’iyyun adawa da kuma aiki da kafofin watsa labarai wajen wayar da kan jama’a, tare da barin kungiyoyin sa-ido kan zabe na duniya su yi ayyukansu yadda ya dace a yayin gudanar da zabuka.
Shi ma shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, wanda mataimakin daraktan watsa labarai na hukumar Nick Dazang ya wakilta, ya bayyana hukumarsa ta fahimci an tafka kura-kurai a zabukan da suka gudana a baya, saboda haka suke kokarin gyarawa. “Kuma ba za a samu nasara ba, dole sai masu zabe sun yi hakurin jajircewa da sadaukar da kai da nuna sanin ya-kamata, yayin zabuka, musamman daga kananan hukumomi”. Inji shi.