✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tashi taron shugabannin APC baran-baram

Taron da shugabannin Jam’iyyar APC na jihohi 36 suka yi da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha a Abuja, ya tashi baram-baram ba tare da…

Taron da shugabannin Jam’iyyar APC na jihohi 36 suka yi da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha a Abuja, ya tashi baram-baram ba tare da cimma matsaya ba a wani muhimmin zama da aka yi a ranar lahadi da ta gabata. Aminiya ta samu labarin cewa har yanzu ba a kawo karshen rikicin da ya dabaibaye Jam’iyyar APC mai mulki ba. Shugabannin Jam’iyyar APC na jihohin sun zauna da Sakataren Gwamnatin Tarayya ne bayan cikar wa’adin da suka ba Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Mista Adams Oshiomhole domin ya duba korafe-korafe da koke-koken da suka gabatar.

A zaman da aka yi, an shafe tsawon sa’o’i ba tare da an cimma matsaya ba.  A takardar da shugabannin jihohin suka sa hannu a kwanakin baya, sun nemi a yaba wa kokarin da suka yi a zaben da ya gabata, kuma sun bukaci a hanzarta cike gurbin tsohon Sakataren Jam’iyyar na Kasa Alhaji Mai Mala Buni, wanda ya zama Gwamnan Jihar Yobe.

Ali Bukar Dolari da Ben Nwoye shugabannnin jam’iyyar a jihohin Borno da Enugu ne ke jagorantar shugabannin, inda suke kukan an jefar da su bayan cin zabe. Rigima a jam’iyyar ta fi karfi a jihohin Katsina da Edo. Sauran korafinsu ya hada da rashin kiran taron Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar da ya kamata a rika yi sau uku a shekara.