✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsare Adam A. Zango kan zargin lakada wa dan jarida duka

A ranar Talatar da ta gabata aka tsare fitaccen jarumi Adam A. Zango kan zargin lakada wa Editan Mujallar Fim, Aliyu Gora duka.Jarumin ya karyata…

Jarumi Adam A. ZangoA ranar Talatar da ta gabata aka tsare fitaccen jarumi Adam A. Zango kan zargin lakada wa Editan Mujallar Fim, Aliyu Gora duka.
Jarumin ya karyata zargin inda ya ce sun cukumi juna ne. Daga baya aka ba da belin jarumin da wadansu mutane hudu.
A ranar Talatar ne editan ya kai karar Adam A. Zango ofishin ‘yan sanda na Metro da ke Kaduna, inda ya ce jarumin ya lakada masa duka a lokacin da ya je Gamji, wurin da Ali Nuhu yake daukar wani sabon fim.
Aminiya ta samu labarin cewa editan ya je wurin daukar fim din ne don ya karbi hotunan bikin gasar City keokle Entertainment Award da aka yi a Legas a makon jiya a wurin Yakubu Mohammed, wanda shi ma yana daga cikin jaruman da za su fito a fim din don zai yi amfani da su a Mujallar Fim.
Editan ya ce: “Bayan na je Gamji ne sai muka yi wasa da dariya, inda bayan na karbi hotunan sai na nufi motata don na koma bakin aikina, kwatsam sai ganin Adam A Zango na yi kamar an jeho shi, bayan ya tsaya a kofar motata ne sai ya fara zagina. Ganin ban ce masa komai ba ne sai ya bude murfin kofata, sannan ya janyo ni waje a lokaci guda ya fara duka na.
“Daga nan sai na tambaye shi me ya sa yake zagina a lokaci guda yake dukana, amma maimakon ya ba ni amsa sai ya ci gaba har ma ya yi mini karo. Da taimakon jama’a aka kwace ni.” Inji Editan.
Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa jarumin yana korafi a kan labarin aurensa na hudu da Mujallar Fim ta buga a watan Yuli 2013, inda ya ce an ci zarafinsa an kuma bata masa suna. “Wannan ta sanya da ya ga Aliyu Gora ya je ya same shi, kodayake ban san me ya gudana har hakan ta kasance a tsakaninsu ba.” Inji majiyar.
Daga nan ne editan ya kai rahoton al’amarin ofishin ‘yan sanda na Metro da ke Kaduna, inda kuma aka gayyaci Adam A Zango don ya yi bayanin abin da ya faru.
A ofishin ‘yan sandan ne sai editan ya ce Falalu dorayi da Fati Ladan da kuma Mustakha Naburaska suna zaginsa hade da yi masa barazana a lokacin da Adam A. Zango yake dukansa.  
Sai dai an yi belin su a ranar Talatar inda kuma suka dawo ranar Laraba aka ci gaba da bincike.
Jarumai da sauran ‘yan fim sun rika ba da baki don a sasanta al’amarin ciki har da Ali Nuhu. Daga bangaren Mujallar Fim kuma akwai Janar Manajar kamfanin da ke buga mujallar Maimuna Alhassan.
A yanzu dai an nemi bangarorin biyu su dawo don a ci gaba da sasanta su a ranar Laraba 31 ga wannan watan.
Bayan sun fito daga ofishin ’yan sandan da misalin karfe 3:30 na yamma ne wakilinmu ya tuntubi editan, inda ya ce shi bai hakura ba kuma ya fi so a bi masa hakkinsa a kotu.
Ya ce: “Ni na kawo kararsa wurin ’yan sanda saboda cin mutunci da ya yi mini. Inda ya buge ni har  ya yi mini karo da kai. Kuma ni ba zan hakura ba amma dai na bar komai a hannun shugabannina sai abin da suka ce. Amma na fi so mu je kotu ta bi mini hakkina.”
Aminiya ta samu labarin cewa sun dauki sa’oi masu yawa a ofishin ’yan sandan don a sasanta su, amma abin ya ci tura.
Adam A. Zango da wakilinmu ya tuntube shi game da zargin da ake masa sai ya ce shi bai bugi editan ba.
“Ni ban buge shi ba amma dai na cukume shi, ya kuma cukume ni. Sai dai kuma ba zan iya cewa komai a yanzu ba sai dai ka neme ni nan gaba domin karin bayani,” inji shi.
Duk da irin kokarin da wakilinmu ya yi don neman karin bayani, amma jarumin ya ki ya ce komai.
Sai dai wani abin mamaki da wakilinmu ya lura shi ne yadda jami’an ’yan sanda suka rika tururuwar zuwa kallon Adamu Zango.
“Tun da nake makaranta nake sha’awar kallon fim dinka,” inji wani dan sanda da yake fada wa jarumin a lokacin da suke zagaye da shi.
Daga nan suka yi masa rakiya zuwa inda ya ajiye motarsa.