✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsare fasto kan yin barazanar aukuwar bala’i ga matar aure

‘Yan sanda a garin Kubwa da ke Birnin Tarayya, Abuja, sun kama wani fasto mai shekara 36 mai suna Melbin Chima da ke Unguwar Gbazango…

‘Yan sanda a garin Kubwa da ke Birnin Tarayya, Abuja, sun kama wani fasto mai shekara 36 mai suna Melbin Chima da ke Unguwar Gbazango a Kubwa bisa zargin yin barazanar aukuwar bala’i ga wata matar aure.

Lamarin kamar yadda Aminiya ta samu labari, ya faru ne a ranar Alhamis din makon jiya bayan samun rashin jituwa a tsakanin mutanen biyu a kusa da wata kotu da ke daura da Babban Ofishin ’Yan sanda.

Bayanai sun ce matar tana kokarin ajiye motarta ce a kusa da inda faston yake zaune a gindin wata bishiya da ke jikin kotun, sai ya mike tsaye ya hau ta da fada tare da zarginta da yunkurin auka masa da mota. Wani dan sanda ya shaida wa Aminiya cewa: “Ya yi ta surutu na aibanta matar, amma a karshe sai ta ce masa surutan da kake ta yi tamkar wauta ce tunda dai ban tanka maka ba ko a sau daya.Bayan ta fito daga cikin kotun ne sai mutumin ya sake tunkararta kan lallai sai ta nemi gafararsa na dangata shi da wauta kuma idan ba haka ba sai ya dauki mataki a kanta saboda shi na kusa da Allah ne (Man of God). Daga nan sai ya dibi kasa a tafin hannunsa ya watsa a gaban motarta tare da barazanar cewa daga lokacin zuwa kwana 3 ba za ta sake tuka motar ba.”

“Wannan ya sa ta shigar da kara a ofishinmu kuma nan take muka kama faston a ranar tare da tsare shi. Mun gurfanar da shi a gaban wata kotun majistire da ke garin Dutse-Alhaji a ranar Litinin kuma bayan sauraron shari’ar sai kotun ta ba da umarnin a ci gaba da tsare shi a Kurkukun Suleja kafin ranar sake zaman shari’ar,” inji dan sandan.

Babban Jami’in ’Yan sandan Kubwa, CSP Ayobami Surajudeen ya tabbatar da faruwar lamarin tare da mika lamarin ga kotun.