An tsare magidanci kan zargin yi wa yara 10 fyade

Wata kotun majistare da ke zama a garin Maraban-Gurku na karamar hukumar Karu a jihar Nassarawa, ta bada umarnin ci gaba da tsare wani magidanci Adamu Umar Dunomo da ake zargi da yi wa yara 10 fyade ta hanyar yin luwadi da su.

Mutumin, wanda dan asalin jihar Yobe ne da ke sana’ar tuki, yana zama ne a yankin Rugar Juli Maraba, inda ya ke tare da matar aure daya da kuma ’ya’ya uku.

Dan sanda mai shigar da kara Nanzing Wilfred ya sanar da kotun a ranar Litinin  cewa, yaran wadanda dukkaninsu maza ne masu shekaru tsakanin 4 zuwa 12, ya na yin luwadi da su ne a gidansa a lokacin da iyalinsa ba ta nan, ko kuma a wani kango da ya ke gina gida a unguwar.

Ya shaidawa kotun cewa ba a kai ga gane lamarin ba sai a kwanan nan bayan daya daga cikin yaran ya kamu da rashin lafiya sannan bayan kai shi asibiti kuma aka gano ya samu wata matsala sanadiyar zakke masa ta dubura.

Alkaliyar kotun mai shari’a Hauwa Onu Osa, ta nemi jin ta bakin wanda ake zargin inda ya musanta lamarin, sai dai da a ka koma bangaren yaran, biyu daga cikinsu tabbatar da yana yi masu fyade.

Kotun ta dage sauraron karar har zuwa ranar 26 ga watan Oktoba, sannan ta ba da umarnin ci gaba da tsare shi a kurkukun garin Suleja.