✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

An tsare mutanen da suka yi fashi a gidan Sanata

Wata Kotun Majistare da ke zamanta a birnin Osogbo, Jihar Osun, ta garkame wasu mutum uku a gidan kaso bisa tuhumar su da yin fashi…

Wata Kotun Majistare da ke zamanta a birnin Osogbo, Jihar Osun, ta garkame wasu mutum uku a gidan kaso bisa tuhumar su da yin fashi a gidan wani Sanata.

Jami’in dan sanda mai shigar da kara, ASP Idoko John, ya shaida wa kotun cewa mutanen da ake zargin sun yi wa mazauna gidan Sanatan Osun ta Yamma, Adelere Adeyemi fashi da misalin karfe 7.00 na ranar 24 ga watan Oktoban 2020.

ASP Idoko ya ce mutanen sun aikata ta’asar a gidan Sanatan ne dauke da muggan makamai da suka hada da adduna, gorori da sauransu.

Ya ce sun yi awon gaba da akwatin talabijin shida da wasu kayayyaki da darajarsu ta kai Naira miliyan biyu, wanda laifin ya saba wa sashe na 1 da na 2 cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Wadanda ake zargin sun ki masa aikata laifin da ake tuhumar su yayin da lauyansu, Taiye Tewogbade ya musanta zargin.