Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
An tsige Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Kano

An tsige Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Kano

‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano sun tsige Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Alhaji Labaran Abdul Madari.

Alhaji Abdul Madari, wanda ke wakiltar Karamar Hukumar Warawa da ke jihar, ya shaida wa BBC cewa ‘yan majalisar tamkar sarakai ne don haka suna da ’yancin cire shi sannan su zabi wanda suke so.

Dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Bunkure, Alhaji Muhammed Uba Gurjiya ne ya gabatar da kudirin tsige shi a zauren majalisar.

Alhaji Uba Gurjiya ya ce batun na da matukar muhimmanci, yana mai yin kira ga ’yan majalisar a karkashin Jam’iyyar APC sun amince da kudirin.

Da yake nuna goyon baya ga kudirin a madadin ’ya’yan Jam’iyyar APC, dan majalisa mai wakiltar Sumaila Alhaji Zubairu Hamza Massu ya ce ’ya’yan Jam’iyyar APC a zauren majalisar sun amince da kudirin tsige Shugaban Masu Rinjayen kuma tuni suka zabi Mataimakinsa Alhaji Kabiru Hassan Dashi a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Ya ce sun kuma zabi Alhaji Tasi’u Ibrahim Zabainawa a matsayin sabon Mataimakin Shugaban Masu Rinjayen na Majalisar.

Wata majiya ta tabbatar wa BBC cewa an cire Alhaji Labaran Madari ne saboda karfin da yake da shi a majalisar wanda wadansu ’yan majalisar ke ganin bai kwanta musu a rai ba.