✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar yarinyar da aka yi wa fyade a makabarta

Jama’ar unguwar Kurmin Mashi a Kaduna sun wayi gari cikin alhini bayan da suka gano gawar wata yarinya mai shekara shida da ake zargin an…

Jama’ar unguwar Kurmin Mashi a Kaduna sun wayi gari cikin alhini bayan da suka gano gawar wata yarinya mai shekara shida da ake zargin an yi wa fyade, aka jefar da gawarta a makabarta.

A ranar Lahadi 10 ga watan Nuwamba ne aka gano gawar yarinyar, wacce bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya mahaifiyarta ta neme ta ta rasa bayan da ta fita waje yin wasa da yara.

Nan take aka bazama neman ta, inda daga baya wani manomi ya gano gawarta an turbude da kasa a cikin makabarta.

Kakakin ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Zuwa lokacin da aka tuntube shi ya ce rundunar ba ta tabbatar musababbin rasuwar yarinyar ba, amma binciken asibiti zai ba da tabbacin dalilin rasuwarta.

“Bayan an kallama bincike, asibiti zai hannanta gawarta ga iyayenta”, inji shi.

Ana iya tunawa wata hudu da suka gabata an gano gawar wata yarinya da aka yi wa fyade a yashe a cikin wani masallaci a unguwar.