✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar mutum biyu bayan ruwan sama a Akwa Ibom

An samu rahoton mutuwar mutum biyu bayan wani ruwan sama mai karfi da aka yi da ya kai awa daya, wanda ya yi sanadiyyar ambaliyar…

An samu rahoton mutuwar mutum biyu bayan wani ruwan sama mai karfi da aka yi da ya kai awa daya, wanda ya yi sanadiyyar ambaliyar a manyan hanyoyin Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.

An gano gawar namiji da mace a cikin kwata a layi mai suna Atiku Abubakar lane kusa da gidan man fetur  na GWT a Uyo. An fara ruwan da misalin karfe 5:30 na yamma zuwa 6:45 na yamma a jiya Lahadi.

Wata ganau mai suna Misis Uduak Mbakara  ta ce, an gano gawar wadanda suka rasun ne a safiyar yau Litinin. Daga nan makwabtan wurin suka sanarwa ‘yan sanda gawar mutanen da suka gani.