Aminiya

An tsinci jariri da ransa a cikin gona a Kudancin Kaduna

A karshen makon da ya gabata ne aka tsinci wani jariri sabon haihuwa da aka yar da shi a cikin wata gona.

Lamarin ya faru ne a garin Gidan Waya da ke Karamar hukumar Jama’a da ke yankin Kudancin Kaduna, kamar yadda shugabar sashen sauraron koke-koke da suka danganci cin zarafin kananan yara mai suna Cibiyar Salama da ke Babban Asibitin Tunawa da Patrick Ibrahim Yakowa da ke garin Kafanchan, Misis Grace Abbin ta shaidawa Aminiya a ofishinta, inda ta ce, lamarin ya faru ne yayin da wata tazo wucewa tare da kawayenta zuwa gona sai ta ji alamar motsi a gefen hanya inda ta leka don duba ko mene ne.

ADVERTISEMENT

“A lokacin har kawayenta na cewa, kada ta leka amma dai ta yi ta maza inda ta ga jariri da ran shi a cikin tsirara. Shi ne aka kawo mana shi kuma likita ya duba ta tare da ba shi magunguna kuma ya tabbatar jaririn bai wuce kwana daya da haihuwa ba a ranar da aka tsince shi.”

“Daga baya mun samu labarin wata yarinya a can yankin Gidan Waya din da ba ta kai shekara ashirin ba da ake zaton ko ita ta yar da jaririyar, amma da muka bincika sai muka fahimci ita kuma labarinta daban ne da wannan domin ita kuma (waccar ‘yar asalin jihar Benuwe ce) ta saki danta ne marar wayo da gangan da nufin bacewa wanda kuma tayi nasarar haka inda shi ma bayan an tsince shi a garin neman wacce ta yar da jaririyar da aka tsinta sai aka gano ita kuma ta yar da danta ne da gangan.”

ADVERTISEMENT

Sai dai a yayin da wakilinmu yake kan hada wannan labari, shugabar cibiyar ta sanar da shi ta wayar tarho cewa, a yammacin jiya an yi nasarar gano wacce ta yar da jaririn tare da wanda ya yi mata cikin, inda a yanzu haka suke tsare a ofishin jami’an tsaron NSCDC da ke kula da shiyyar Kudancin Kaduna da ke garin Kafanchan.

“A yau muke sa ran kawo mana su don yi musu wasu tambayoyi.” Ta bayyana.

Ta ce, ya zuwa yanzu da mutane suka fara gane cibiyar su, sun samu koke-koke iri daban-daban guda (116) da ya kunshi cin zarafin yara kanana da kuma fyade da danginsu, wata shida da bude cibiyar.