✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci yarinya a gefan rafi tsutsotsi na fita a jikinta

A karshen makon da ya gabata ne aka tsinci wata yarinya da aka kiyasta shekarunta ba su wuce hudu a gefan wani rafi da ake…

A karshen makon da ya gabata ne aka tsinci wata yarinya da aka kiyasta shekarunta ba su wuce hudu a gefan wani rafi da ake kira Wawan Rafi da ke kusa da garin Zangon Kataf da ke jihar Kaduna matashiyar tsutsotsi na fita ta al’aurarta.

Lokacin da Aminiya ta isa babban asibitin garin Zangon Kataf, inda aka kaita don lura da lafiyarta, babu wanda ya san labarinta.

“An bincika kauyen da Wawan Rafi ya ke babu wanda ya iya gano yarinyar. Mutane sun yi ta zuwa asibitin don duba ta amma har yanzu babu wanda ya gano ko daga ina take ballantana sanin ko me ya faru da ita.” Inii, wani a asibitin da ya ke yi wa Aminiya karin bayani. Ya ce yadda aka same ta al’aurarta a lalace har tsutsotsi na fitowa ta gabanta ya sa ana zargin ko dai fyade aka yi mata ko kuma aikin matsafa ne. “Wallahi wanda ya dauko yarinyar nan ma ya yi kokari domin idan tsoro bai hanaka taba yarinyar ba to kyama ba zai bar ka ka taba ta ba, amma haka wannan dan talikin ya dauko ta zuwa asibitin. Mu muna ganin idan ba iyayenta ne suka jefar da ita saboda wata lalura ba to zai iya zama wasu ne suka dauke ta suka lalata ta har ta kai ga haka sannan su ka yasar da ita ko kuma tunaninmu na karshe shi ne watakila matsafa ne suka yi nufin wani abu da ita Allah Ya kubutar da ita.

Allah ne kawai masani amma a nan ba mai iya fada maka gaskiyar abin da ya faru tunda babu wanda ya tsinto ta kuma babu wanda ya san ta, sannan yarinyar ba ta fara yin magana yanzu ba saboda galabaitar da tayi.” In ji shi.

Daga baya an ce shugaban Karamar Hukumar ya turo an dauketa zuwa wani asibiti dabam da ba a san ko wanne ne ba, kamar yadda wani ma’aikacin asibitin da bai so a bayyana sunansa ba ya shaidawa Aminiya.