Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
An tura malamin makarantar Daura kurkuku

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Katsina a Fadar Sarkin Daura

An tura malamin makarantar Daura kurkuku

Bayan ’yan sandan sun gabatar da Malam Bello Abdullahi mai shekara 78 da Habibu Bello mai shekara 28 da Abba Abubakar mai shekara 16 a kotu bisa zargin kuntata wa almajiran da suke makarantarsu a Daura, lamarin da ’yan sanda suka ce ya saba wa sashe na 97, 257 (b) da 238 na kundin  Final Kod, Mai shari’a Nuraddeen Abdullahi ya ba da umarni a ajiye wadanda ake zargin a gidan yari zuwa ranar 22 ga Oktoba domin ci gaba da sauraron karar.

…An sake kai wani samame kan makarantar allo a Katsina

A wani labarin kuma, Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina ta ce jami’anta sun kai samame a wata makarantar allo da ake daure almajirai da mari a birnin Katsina, inda ake zargin an tsare mutane da dama.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa an kama malamin makarantar mai suna Malam Salisu Hamisu.

Da Aminiya ta ziyarci makarantar da ke Kofar Durbi, ta samu ’yan sanda zagaye da makarantar, sannan akwai wata makarantar da ke kusa da wannan, wadda ita ma ’yan sanda suka mamaye.

Makwabtan makarantar sun shaida wa Aminiya cewa makarantar ta fi shekara 15 tana gyara halayen kangararrun yara kuma ana koyar da karatun Kur’ani.

Tuni manyan malaman Musulunci suka zauna da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar kan lamarin, inda majiyar Aminiya ta tabbatar da cewa Kwamishinan ya shaida wa malaman irin cin zarafin yaran da ake yi a makarantun.

Wata majiya ta ce tuni Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a fara binciken irin gidajen kula da kangararrun yaran a duk fadin kasar nan tare da gurfanar da masu azabtar da yaran a gaban kotu.