✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tura ’Yar shekara 14 wakafi kan zargin kisan ’yar kishiyarta

A kwanakin baya ne aka tsare wata yarinya ‘yar shekara 14 mai suna Hannatu Ibrahim (Ba sunanta na ainihi ba) watanni hudu a gidan kangararrun…

A kwanakin baya ne aka tsare wata yarinya ‘yar shekara 14 mai suna Hannatu Ibrahim (Ba sunanta na ainihi ba) watanni hudu a gidan kangararrun yara na Bauchi bisa tuhumarta da kashe ‘yar mijinta mai shekara daya, wacce kishiyarta da aka sake ta ta ji haushi ta dawo da ita gidan mijin a Nasaru karamar Hukumar Ningi ta Jihar Bauchi, lokacin da yarinyar ke fama da rashin lafiya sai ta rasu. Limamin masallacin Juma’a na Gwallaga da Lauya Garba Hassan da Shugabar kungiyar Mata Zawarawa da marayu ta Jihar Bauchi Hajiya Sa’adatu Umar sun nemi belin yarinyar, wakilinmu ya bi diddigin labarin kamar haka:

Auren dole aka yi mini ina da shekara 14
Da Aminiya ta bukaci “Hannatu” ta bayyanan mata dalilin ajiye ta a wannan gida da ake tsare yara sai ta ce, “Yarinyar mijina ce ba ta da lafiya a wajen uwarta sai ta dawo mini da ita, bayan uwar ta bar gidan. Yarinyar ta kwana tana kashin jini da amai, sai ta bata mini kayan gadona, shi ne na saukar da ita kasa, sai uban ya dauke ta yakai ta asibiti, sai aka tura su asibitin Birnin Kudu suka yi kwanaki hudu, daga can suka tura su Kano, sai ta rasu. Bayan rasuwarta da kwana biyu uwar da wata ‘yarta a Ningi suka zo gidan suna zagina, suka ce ba za su yarda ba, mahaifiyata ta ji labari ta ce na koma gida, da sassafe sai ta zo gidanmu da wuka ta ce sai ta kashe ni. Mutane suka taru suka ba ta hakuri, sai ta kai kara Ningi ta ce wai na tattaka cikinta na fasa mata hanta, alhali ni ban aikata haka ba, tare kuma da jin zafin an sake ta kafin zuwana gidan ta kawo min yarinyar na tausaya na rike ta. Da wannan abu ya faru suka kai ni ofishin ‘yan sanda na Ningi na kwana hudu, aka yi ta azabtar da ni, aka kai ni ofishin CID na Bauchi na kwana biyu, daga can suka kai ni kotun majistare, shi ne aka kawo ni wannan gida, kusan watanni hudu ke nan. Daga can kuma aka ci gaba da kai ni babban kotu (High Court).’’
Ta bayyana cewa tana da shekara 14 aka yi mata aure, ‘’lokacin da na je garin iyayena Nasaru sai ya ganni ya ce yana so, ni kuma lokacin na samu makarantar sakandare a Bakari Dukku zan fara, shi ne iyayena suka amshe ni a hannun uwar goyona, suka ce na girma, sai suka aurar masa da ni ba tare da ina so ba. Kishiyar tawa kafin ya auro ni ya sake ta, amma tana zagina, tana cewa sai ta yi maganina tunda na aure mata miji. Kuma akwai lokacin da take zuwa gidan su shiga dakina su kore ni, su yi ta hira da shi, ni kuma sai na fita na barsu, idan sun gama sai na dawo. dakinsa daya ne, yana korarta sai aka sanya ni ciki. Kuma tunda nake zaune da wannan mutum tsawon watanni biyu sau biyu ya taba kwana a gida, idan mangariba ta yi abokansa sukan zo su fice sai asuba yake dawowa gida, ban san inda yake tafiya ba, wadanda muke zaune gida daya duk sun san wannan.’’
“Ganina ya yi ya nema wajen kawuna don ba na so dama aka yi auren, ba shi da wata sana’a ta arziki, idan sharri na yi masa hukuma ta je Nasaru ta tambaya, tun daga fada kowa ya san ba shi da sana’ar kirki. Lokacin da za a yi auren ma babu irin kukan da ba mu yi ba ni da mahaifiyata, har ta buga wa uwar goyona ta je ta dawo da ni Bauchi, amma duk da haka suka amshi sadaki suka daura aure suka zo suka tafi da ni. Ni yanzu fatana a lura da wahalar da na sha a hannun wannan mutum kuma na dauki lamarin a matsayin kaddara, don haka me yarinya ta yi min da zan kashe ta? A taimaka mini a sake ni na koma hannun uwar goyona na ci gaba da karatu, wadanda suka ja mini wannan wahala da azaba na barsu da Allah. Shi ma da matarsa na barsu da Allah. Saboda tunda ya sa aka kama ni ya tafi ya mayar da matarsa ta ci gaba da zama a dakina da kayan dakina. Kuma ya biya ni kayana da ya kwashe ya ba ta, saboda bai taba zuwa ko sau daya don ya ji me ake ciki ba.’’
Ta yi nuni da cewa, ‘’tunda ya kawo ni bai ce ya sake ni ba, bai ce yana aurena ba, sai ya maida matarsa, an raba ni da karatuna, an hana ni ‘yanci, ni kuma ba da zaman aure ba, da fatan wadanda za su iya za su taimaka mini. Kuma a kan kayana ma babu irin zagin da bai yi wa iyayena ba, har ya yi musu barazanar idan ba su fita harkarsa ba sai ya yi maganinsu. Wannan aure kanen babana ya kulla, babana da mamana ba sa so, kuma loakacin da aka kai ni Ningi ya hana babana zuwa, ya ce idan ya je za a kama shi.’’

An fi karfina ne a kan lamarin
Maryam ita ce uwar goyon Hannatu, ta bayyana wa Aminiya cewa, “wannan yarinyar ‘yar kanina ce, tun tana karama nake rike da ita, saboda ban samu haihuwa ba, ubanta ya ba ni na goya, amma lokacin da aka yi mata aure, kishiyarta Shamsiyya ta dawo mata da yarinya, alhali lokacin wannan aure sai da aka yi yarjejeniyar ba za a dawo mata da yarinya ba, saboda dama an ji uwar yarinya na cewa idan ta shiga dakinta za ta dawo mata da yarinya, wannan yarinya ba ta mallaki hankalinta ba. Kuma sanin kowa ne yarinyar ba ta da lafiya kafin aka kawo ta, da ta yi mata kashi sai ta ajiye ta a kasa, uban ya zo ya same ta ya dauka ya mayar wa uwar. Da farko ba ta son wannan auren, na sanya ta a makaranta har ta gama firamaren Unguwar Borno ta samu Sakandaren Bakari Dukku, amma shi kanen uban Jamilu ya ce dole sai ya cire ta ya yi mata aure.’’
Ta ci gaba da cewa, “na hana auren, na ce tunda a Bauchi akwai masu sonta a barta ta fitar da mutum guda ta yi aure ta ci gaba da karatu, kanen ubanta ya ce ya yi niyya babu mai hana shi, ya nuna min ban haifa ba, yanzu da abu ya baci kowa ya kauce ni kadai nake kaiwa da komowa. Lamarin kamar akwai manufa, sai yarinyar ba ta da lafiya take kawo ta, idan ta warware sai ta zo ta dauke ta, har wannan abu ya faru. An kai ta ofishin Area Command a Ningi ba ta san yadda za ta kare kanta ba, da ta sha duka da azaba ta tsorata ta ce ita ta kashe ta! Kuma tunda aka tsare ta mijn bai taba zuwa ba, na ki wannan auren saboda mijin ba shi da kamun kai, ba shi da sana’ar arziki.’’
Dangane da yadda aka yi ta san haka sai ta ce, “Ni ko na sani, tunda ina Nasaru garin iyayena ne can na tashi, mijina yayan Malam Ibrahim Idris Limamin Gwallaga ne ya auro ni, sai Allah Ya yi masa rasuwa, shi ne na kama haya nake zaune a wannan gida tare da yarinyar .’’
Ta ce, ‘’Mun je kotun Game billage ya kai sau uku, High court sau hudu. Gaskiya ban ji dadi ba, saboda mijinta bai tsaya ba, kowa ya kauce. Su uku ne a kurkuku, akwai yarinyar da ta mari abokiyarta ta rasu a bayan fada, akwai yarinyar da ta haihu ita da uwar suka kashe dan, duk tare suke, amma an bayar da belinsu saboda suna da tsayayyu, ita kuwa har yanzu, to me mutum zai ce da fadan da ya fi karfinsa?.’’
Wakilinmu ya zanta da babban jami’in gidan tsare yara da ke Bauchi Musa Zailani Jama’are, wanda ya ce kotun majistare ta biyu ta kawo musu yarinya su ajiye, don haka su ajiya ce kurum tasu, a duk lokacin da kotu ta kawo takardar beli sai su sake ta, idan ba haka ba tana nan har sai ta kai shekaru 18 sai a mayar da ita gidan yari.
Ya ce akwai rashin gata cikin lamarin, saboda ita kanta ba ta mallaki hankalinta ba balle a ba ta jinya. Kuma mutuwa ko a hannun waye za ta iya aukuwa, akwai rashin adalci na mijinta, saboda sun sha buga masa waya don ya zo a tafi kotu tare da shi amma sai ya yi ta zage-zage ya ce babu ruwansa, don haka suka fahimci kamar yana da matsala suka daina kiransa, saboda akwai lokacin da ya ce idan ya so da zai iya sa a kashe ta kamar yadda ta kashe ‘yarsa, don haka muka rabu da shi, saboda mun fahimci ya jahilci shari’a.

Mun yi kokarin sasanta maganar amma mijin ya ki
Maryamu Babayawo uwar goyon Hannatu– Garba Idi
Wakilinmu ya je Nasaru ya samu Malam Garba Idi, wanda shi ne Ciroman Nasaru kuma wakilin Sarkin Nasaru, wanda ya bayyana cewa tun farkon maganar sun yi kokarin sasanta su tun ba a je kotu ba, amma mijin ya ki amincewa, don haka suka koma gefe, saboda sun fahimci akwai rashin kunya irin ta matashin kauye tare da shi.
Ya kara da cewa, sun yi kokarin wayar masa da kai domin ya fahimci cewa idan hukuma ta gano gaskiyar maganar shi da mahaifiyar yarinyar ya kamata a tuhuma, saboda sai idan yarinyar ba ta da lafiya ake kai ta, ga kuma batun auren dole da auren wuri da cire yarinyar a makaranta, wanda a yanzu gwamnati na kyamar hakan. Bayan haka tunda aka kai yarinyar kotu aka tsare ta ya dawo ya mayar da matarsa suka ci gaba da zama. Kuma uban matar da farko ya ki sake daura musu aure, saboda ya ce aure ya haramta tsakaninsu amma ya je wani wuri aka mayar musu da auren, suka koma dakin yarinyar suka mallake kayanta yanzu suke zaune.
Wakilinmu ya nemi mijin yarinyar watau Musa don jin ta bakinsa amma ya ce ba ya gari, daga karshe ya rufe wayarsa. Kuma duk an zaga inda ake zaton za a same shi amma ba a iske shi ba.
Washegari Ciroma ya buga wa wakilinmu waya ya sanar da shi cewa sun isar da sakonsa ga mijin matar amma ya ce shi ba zai je kotu a Bauchi ba, sai dai zai gaya wa matarsa idan ta ga za ta iya zuwa, domin ita ce ta yi kara, amma shi babu ruwansa.
Shugabar kungiyar mata zawarawa da marayu Hajiya Sa’adatu Umar, ta ce za su ci gaba da gwagwarmayar bin shari’ar har sai sun ga an bayar da belin yarinyar, kuma za su yi karar mijin da matarsa don a bi hakkin yarinyar. Ta ce za ta je hukumar bayar da taimakon lauya (Legal Aid Council) da ke Bauchi don neman taimakon lauyoyi.
Rijistaran babbar kotu ta biyu Barista Mohammed Zakari Ya’u, ya bayyana cewa, a ranar 26 ga watan Satumba suka samu takardar neman belin Hannatu daga Lauya Garba Hassan, saboda kotun majistare ta biyu ba ta da hurumin bayar da belin abin da ya shafi kisan kai.
Ya ce, Mai shari’a Bitrus Sanga ya saurari maganar, amma ba a tsara karar a kan ga laifi takamaime da ake tuhumarta ba, haka kuma masu kara ba su bayyana a gaban kotu, don haka suka rubuta wa ma’aikatar shari’a domin su tuntubi ‘yan sanda a bincika a yi wa babbar kotun bayani. Idan ma’aikatar shari’a ta fahimci ‘yan sanda da masu kara ba su da gamsasshen bayani kan tuhumar da ake yi wa Lawiza kotu za ta iya bayar da belinta.