Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An yanka yarinya `yar shekara 5 a Kebbi

Wani ya yanka wata yarinya  `yar shekara biyar a unguwar Rikito a garin Zuru da ke jihar Kebbi. An yanka yarinyar ne lokacin da take kwance a wajen harabar gidan su saboda yanayin zafi.

Wani da ba a tantance kowaye ba ya dauki yarinya da nufin tafiya da ita zuwa wani wuri.

ADVERTISEMENT

Majiyarmu ta samu rahoton cewa, yarinyar na kwance ne kusa da kakarta, sai wani ya yazo ya dauke ta da gudu hakan yasa matar ta kwarma ihu, daga sai mutumin ya jefar da ita ya gudu. An samu yarinyar a yanke, kamar yadda makwabtan gidan suka sanar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Kebbi DSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da aukuwar hakan kuma ya ce, hukumar `yan sandan na ci gaba da binciken lamarin.

ADVERTISEMENT