✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa magidanci hukuncin kisa

Babbar Kotun Jihar Kano ta 3 ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani magidanci mai suna Abba Mustapha bisa samunsa da laifin…

Babbar Kotun Jihar Kano ta 3 ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani magidanci mai suna Abba Mustapha bisa samunsa da laifin hallaka wani mutum mai suna Buhari Abubakar ta hanyar yi masa dukan kawo wuka.

Tun a shekarar 2014 ce ake zargin Abba Mustapha mai kimanin shekara 33 da kashe marigayin inda ya dauki fartanya ya kwada wa marigayin a sassan jikinsa bayan wani sabani da ya shiga tsakaninsu inda Buharin ya fadi daga bisani ya ce ga garinku nan.

Da yake yanke hukunci Alkalin Kotun Mai shari’a Ahmad Tijjani Badamasi ya ce laifin da wanda ake zargin ya aikata laifi ne da ya saba wa sashe na 221 na Kundin Final Kod.

Mai shari’a A.T. Badamasi ya  ce lauyan gwamanti Barista Zakariyya Muhammad Garba ya gabatar da shaidu kwarara wadanda suka gamsar da kotu cewa lallai Abba ya aikata wancan kisan kan don haka ya yanke masa hukuncin kisa.