✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa matar da ta kashe makwabciyarta hukuncin kisa

A ranar Talatar makon jiya babbar kotun da ke zama a Ikeja a Legas ta yanke wa matar da ta kashe makwabciyarta a Unguwar Ajegunle…

A ranar Talatar makon jiya babbar kotun da ke zama a Ikeja a Legas ta yanke wa matar da ta kashe makwabciyarta a Unguwar Ajegunle hukuncin kisa.

Kotun ta samu matar mai suna Stella Gilbert mai shekaru 36 da laifin kisan makwabciyar ta Stalla Godwin lokacin da rikici ya kaure a tsakaninsu biyo bayan takaddamar su akan waye zai gaje teburin zama da wani makwabcin su da ya ta shi ya bari a gidan da suke haya.

Makwabtan biyu na hayar daki guda dai-dai ne a gidan inda rikici ya kaure a tsakanin su akan teburin zaman inda Stella Gilbert ta dabawa makwabciyar ta Stella Godwin wuka a kirji da bayanta lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ta.

 Stella Gilbert a lokacin da aka fito da ita daga harabar kotu bayan an yake mata hukuncin kisa
Stella Gilbert a lokacin da aka fito da ita daga harabar kotu bayan an yake mata hukuncin kisa

Mai shari‘a Raliyatu Adebiyi, ce ta yanke wa Stella Gilbert hukuncin kisa bayan da ta yi watsi da ikirarin ta na cewa, ta yi hakan ne domin kare kan ta, ta ce mai laifin ta yi amfani da wuka ne wanda makami ne mai muni ta kuma daba wa marigayiyar a kirji, inda anan zuciya take wajen da ke da babban hadari, ”Hujjojin da aka tattaro daga shaidu wadanda suka hada da dan uwan marigayiyar da kuma mijinta tare da ‘yar sanda sun tabbatar da ta soki marigayiyar a kirji ne“. In ji ta.

Ta ce, wannan lamari ’yar manuniya ce da ke nuna bukatar kyautata zamantakewar masu zaman gidan haya a birnin Legas.

Stella Gilbert ta fadi kasa inda ta yi ta birgima a lokacin da ta ji hukuncin da mai shari’ar ta yanke mata, inda ta nemi sassauci ta kuma nemi a yi mata rahama.