✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa Tsohon Gwamnan Abia hukuncin dauri shekara 12

A yau Alhamis wata babbar kotu a Legas ta yanke wa Sanata mai ci kuma tsohon Gwamnan jihar Abia, Orji Uzo Kalu hukuncin zama a…

A yau Alhamis wata babbar kotu a Legas ta yanke wa Sanata mai ci kuma tsohon Gwamnan jihar Abia, Orji Uzo Kalu hukuncin zama a gida kaso na tsawon shekara 12 saboda zargin almundahanar Naira biliyan 7.2.

Ana tuhumar Orji Uzo, da laifuka 39 bayan Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotun.

An yi sharia’r Uzo Kalu ne tare da kamfaninsa Slok Nigeria Limited ne da kuma tsohon Kwamishinan  kudi na jihar Abia a lokacin da Mista Kalu ke Gwamna.