✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yankewa matar da ta kashe mijinta hukuncin kisa ta hanyar rataya

Wata babbar kotu a Kano ta yanke hukuncin kisa akan matar da ta hankado mijinta daga saman bene lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa a…

Wata babbar kotu a Kano ta yanke hukuncin kisa akan matar da ta hankado mijinta daga saman bene lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa a gidansa da ke unguwar Dorayi a birnin Kano.

Matar mai shekara 35, mai suna Rashida Sa’idu an kamata da laifin kisan kai wanda ya sabawa sashi na 221 na kundin dokar.

Lauyar da ta gurfanar da mai laifin mai suna Maryam Jubrin, ta shaida wa kotun cewa matar ta aikata laifin kisan ne a ranar 25 ga watan Fabarairun shekarar 2019 da misalin karfe 8 na dare inda bayan da fada ya kaure a tsakaninta da mijin ta mai suna Adamu Ali, wanda take zargi da neman mata a lokacin da yake magana a wayar salula a gidansu da ke Dorayi inda ta turo shi daga saman matattakalar bene lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Lauyar wacce tazo da shaidu 4 suka bada shaida akan kisan, ta ce kafin rasuwarsa marigayin malami ne a kwalejin horar da malamai ta tarayya da ke Kano

A daya bangaren Iliya Dauda, lauyan da ke kare wacce aka yankewa hukuncin yazo da shaidu mutum biyu da suka bada shaidar sabanin kisan, sai dai Alkalin Kotun Mai Shari’a A.T. Badamasi, ya gamsu da cewar wanda matar ta ce ta kashe mijinta, ” An yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.” In ji shi.