Aminiya

An yi arangama tsakanin ‘yan Kwankwasiyya da Gandujiyya a Kano

Akalla mutum takwas ne suka samu raunuka yayin da aka lalata motoci 10 a yau Litinin lokacin da aka yi wata arangama tsakanin kungiyar magoya bayan Kwankwasiyya da Gandujiyya a jihar Kano.

Majiyarmu ta samu rahoton  cewa, an yi arangamar ne a wata karkashin wata sabuwar gada da ke hanyar garin Madobi zuwa cikin birnin jihar

ADVERTISEMENT

Alhaji Sanusi Bature Dawakin Tofa, Kakakin dan takarar Gwamnan jihar Kano na PDP Injinya Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da yin arangamar tsakanin magoyan biyu a yau Litinin.

Alhaji Sanusi, ya kara da cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:15 na rana, lokacin da ‘yan Kwankwasiyya ke dawowa daga Karamar Hukumar Madobi tare da shugaban sun a Kasa Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, bayan kaddamar da sabuwar Kwalejin mata ta unguwar zoma da aka gina.

ADVERTISEMENT