Da Dumi Dumi

An yi barazanar korar Indiyawan da ke zaune a Najeriya

Wani karamin jakadan Najeriya da ke Jihar Goa da ke Kudancin Indiya, ya yi barazanar korar daukacin Indiyawan d ake Najeriya, matukar ’yan sanda suka ci gaba da korar ’yan Najeriya daga gidajen da suke haya.
Da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Indiya (IANS), bayan ya kammala ganawa da ’yan Najeriya, Jami’in Difulomasiya Jacob Nwadadia, ya bai wa Gwamnatin Jihar Goa wa’adin daina korar ’yan Najeriya daga gidajensu ba bisa ka’ida ba.
“Akwai ’yan Najeriya kimanin dubu 50 da ke zaune a India, amma Indiyawan da ke zaune a Najeriya sun kai miliyan daya. Don haka za a koro dubban ’yan Najeriya, matukar ba a daina korar ’yan Najeriya daga gidajensu ba,” inji shi.
Gwamnatin Jihar Goa ta bayar da umarnin a kori bakin haure da ke zaune a wannan gari da ake zuwa yawon shakatawa, bayan da fataken kwaya suka yi artabu da ‘yan Najeriya kimanin mutum 200. Su ma ’yan sanda da ’yan garin sun kara da ’yan Najeriya.
’Yan Najeriya sun yi zanga-zanga, bayan da aka kashe mutum daya daga cikinsu, suka dauko gawar suka sauketa a kan babban titi da ake kira National Highway 17, inda suka bukaci jami’in difulomasiya ya zo a yi binciken musababbin abin da ya kashe dan Najeriyar. A lokacin karon battar ’yan Najeriya sun lalalata motocin ’yan sanda, sannan suka yadda gawar dan uwansu a tsakiyar titi, inda suka tare motoci masu wucewa.
Shi kuwa babban Ministan Jihar, Manohar Parrikar, ya yi ikrarin cewa, an halaka dan Najeriyar ne a lokacin da kungiyar fataken kwaya suka yi karon batta da juna, amma ’yan Najeriyar sun bayyana cewa fataken kwayar jihar ne suka kashe musu dan uwa. Ministan ya koka kan cewa mafi yawan ’yan Najeriyar da ke zaune a Goa hoton fasfo dinsu da na izinin shiga kasar kawai suke rike da shi.
Chioma Ghansoli, ’yar shekara 24, wadda ke da zama a Anjuna, na daya daga cikin wadanda ke fuskantar barazanr kora daga gidajensu. Wanda ya ba ta haya ya umarceta da ta fice daga gidansa.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya