An yi bikin karrama ’yan fim a Kano

A ranar Talatar da gabata ce aka gudanar gagarumin bikin karrama ’yan fim da aka dade ba a yi irinsa ba a Jihar Kano.

Taron karramawar, wanda aka yi wa lakabi da ‘Walwanne 2019 Kannywood Award’ Kamfanin Walwanne ne ya dauki nauyin shiryawa, kuma ya samu halartar mutane da dama, duk da cewa an yi shi ne bisa tsarin gayyata. Kuma mai gabatarwa shi ne Alhaji Shehu Hassan Kano.

Tun farko, jagoran shirya taron karramawar, Abubakar Bashir Maishadda ya sako wani faifan bidiyo inda yake murna yana nuna yadda mutane suka amsa kiran halartar taron.

A babban matakin karramawar, an karrama tsohon jarumi, Alhaji Hamisu Iyantama da kyauta ta musamman ta Life Achiebment. Sai kuma Daraktan Shekarar 2019, wanda Darakta Kamal S. Alkali ya lashe sai kuma mawaki Nazifi Asnanic da ya lashe furodusa na 2019.

A matakin jarumai kuwa, Jarumi Umar M. Shareed ne ya lashe kyautar Jarumin 2019 da fim din Mansoor, Hassana Muhammed wadda ta fito a fim din Hauwa Kulu ta lashe kyautar Jarumar 2019.

ADVERTISEMENT

A bangaren mawaka kuma, mawaki Ado Gwanja ne ya lashe kyautar Mawakin 2019.

Haka kuma, a bangaren wadanda ba a ciki gani ko jinsu ba a harkokin fim, kasancewar ayyukansu na bayan kyamara ne a  karramawar ba a bar su a baya, domin Sani Candy ne ya lashe kyautar wanda ya fi iya tace murya na 2019, Aminu Mu’azu Medisuitetb kuma ya lashe kyautar Editan Bidiyo na 2019.

Bikin ya samu halartar manyan jarumai da daraktoci, kamar su Abba El-Mustapha da Yaseen Auwal da Kamaye na shirin Dadin Kowa da Ali Nuhu da Baballe Hayatu da Darakta Sheikh Isa Alolo da sauransu.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya