Da Dumi Dumi

An yi garkuwa da Alkalin Kotun Daukaka Kara

Sufeto Janar na ‘Yan sanda Mohammed Adamu
Sufeto Janar na ’Yan sanda Mohammed Adamu

‘Masu garkuwa da mutane sun sace wata Alkalin Kotun Daukaka Kara a Jihar Edo Mai shari’a Chioma Nwosu-Iheme. Masu garkuwa da mutane sun kuma bindige dan sandan da ke yi mata rakiya.

Shaidu sun ce wadanda suka sace Mai shari’a Chioma Nwosu-Iheme sun kai mata hari ne a wata mota kirar Toyota Boltron kuma sun yi garkuwa da ita ce a kan hanyar Benin zuwa Abgor a kusa da cocin Christ Chosen Church lokacin da take kan hanyarta ta zuwa Abuja.

Shaidun sun ce “Masu garkuwa da mutanen sun bude wuta ga motar alkalin inda suka kashe dan sandan da ke yi mata rakiya bayan sun sha gaban motar da alkalin take ciki.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Edo Mohammed Dan Malam ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce “An dauki matakan tsaro domin kubutar da ita.”

Wannan lamari yana zuwa ne a daidai lokacin da masu garkuwa da mutane suka sako wani limamin addinin Kirista mai suna Fada Arinze Madu da suka sace a ranar Litinin da ta gabata a Jihar Enugu

ADVERTISEMENT