✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake a Zamfara

Maharan sun rika harbe-harbe cikin iska inda daga bisani kuma suka cika cika bujensu da iska.

Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutum bakwai ciki har da wani hakimi a Karamar Hukumar Anka ta Jihar Zamfara.

Wani ganau da gidan rediyon Freedom ya ruwaito, ya ce bayan maharan sun dauki mutanen a daren Juma’a, sun yi ta harbe-harbe a iska kafin daga bisani su cika bujensu da iska.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, SP Shehu Muhammad ba saboda bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma barayin shanu.

A makonnin baya gwamnan Jihar, Muhammad Matawalle ya samu amincewar daukar mutum 7,500 ’yan jihar da za su yi aikin dan sanda a cikin al’ummomin jihar.

Idan ba a manta ba a makon jiya Aminya ta kawo rahoto cewa rukunin farko na jami’an tsaro na musamman din da aka tantance sun tafi makarantun horas dan kuratan ’yan sanda da ke Sakkwato da Kaduna inda za a ba su horo na wata biyu.

A watan Disamba ne ake sa ran jami’an tsaron na musamman za su fara aiki a jihar ta Zamfara kuma gwamnatin jihar ce za ta rika biyan su albashi.

A jawabinta kafin a debi kuratan zuwa cibiyoyin da za a horas da su, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ce mutanen za su yi rika sanya kayan sarki kuma za su yi aiki ne da ofisoshin ’yan sanda a fadin jihar.

Ta bayyana cewa hikimar daukar su ita ce su ne,  a matsayin wadanda suka taso a cikin unguwanni da yankunan jihar za su iya saurin gano take-taken bata gari domin a dauki mataki da wuri.