✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da likitoci biyu da ma’aikacin asibiti a Benuwe

Masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa sun yi garkuwa da wasu likitoci biyu da karin ma’aikacin asibiti guda a ranar Alhamis din da…

Masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa sun yi garkuwa da wasu likitoci biyu da karin ma’aikacin asibiti guda a ranar Alhamis din da ta gabata a kan hanyar Ichama-Okpoga a karamar hukumar Okpokwu da ke jihar Benuwe.

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun yi  garkuwa da mutanen uku dukkansu ma’aikatan asibitin Okpoga a lokacin da suke kan hanyar su daga wajen aiki, zuwa yanzu masu garkuwar sun fara tuntubar dangin daya daga cikin likitocin inda suke neman a basu kudin fansar sa Naira miliyan 10.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a Jihar Benuwe DSP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce jami’an rundunar sun tunkari lamarin sai dai bata yi bayanin ko masu garkuwan sun tuntubi dangin wadanda aka sace ba.

Ta ce, jami’an ‘yan sanda na bincikar lamarin inda ta bayyana yankin Okpokwu da Ado da yankuna masu sarkakiya da ake fuskantar kalubalen tsaro.