✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da mahaifiyar tsohon kocin Super Eagles

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Samson Siasia a jihar Bayelsa. Mahaifiyar tsohon kocin mai suna…

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Samson Siasia a jihar Bayelsa.

Mahaifiyar tsohon kocin mai suna Misis Beauty Ogere Siasia, mai shekaru 76 an sace ta ne da misalin karfe 2 na tsakar daren yau Litinin a gidanta da ke unguwar Odoni a Karamar Hukumar Sagbama da ke jihar Bayelsa.

Wannan shi ne karo na biyu da ake yin garkuwa da mahaifiyar Kocin. A shekarar 2015 ‘yan bindigar suka yi garkuwa da ita, inda har sai da tayi kwanaki 12 kafin a sako ta daga hannun masu garkuwa.

Kakakin Hukumar ‘yan sandan jihar SP Asinim Butswat, ya ce yanzu haka jami’an ‘yan sandan jihar na ci gaba da bincike a unguwar Odoni don kubutar da Misis Beauty Ogere Siasia.