Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An yi garkuwa da mai jego da ’yan mata 4 a Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i

Wadansu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mata hudu ciki har da mai jego a Unguwar Rigasa da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 1:48 na dare ranar Talatar da ta wuce ya yi matukar tayar wa da mazauna yankin hankali.

ADVERTISEMENT

A cewar mijin mai jegon, Ibrahim Abdullahi yana kwance sai ya ji ’ya’yansa na fada masa cewa wadansu mutane na buga kofar gidansa.

Ya ce da ya tashi sai ya duba agogonsa ganin cewa kusan karfe biyu saura ne na dare sai hankalisa ya yi matukar tashi. Bayan ya gudu ne sai ya ji sun shiga gidan har sun dauke masa mata.

ADVERTISEMENT

“Da na duba lokaci ne sai na gigice su kuma barayin suna ta cewa a bude musu kofa tare da yin suratai ba su ma damu ba kuma sai harbi suke yi. Daga baya da na ji sun dauke min mata sai na fara kuka kuma a yanzu haka matar tana hannunsu amma jinjirar da sauran yaran nawa suna makwabta,” inji shi.

Wata budurwa  mai suna Fatima Ibrahim wadda ta kubuta daga hannun masu garguwa da mutanen ta bayyana yadda ta kubuta, inda ta ce, “Lokacin da suka shigo gidanmu sai suka ce da Antina ta ba su wayar hannunta, da ta mika musu sai suka ce in taso in bi su. Daya ya ce in sa takalma, da na bi su zuwa waje sai yake tambayata me nake da shi na ce babu komai. Ya sake tambayasta me nake sayarwa? Na ce babu komai.   Sai ya ce to, yanzu me nake so su yi mini sai na ce don Allah su yi hakuri su kyale ni. Daga nan sai ya buga min bindiga kuma ya ce kada na yi ihu, ni kuma saboda zafi sai na kwala ihu.”

“Daga nan sai wani mutum daga nesa ya ce su wane ne nan? Sai daya daga cikinsu (barayin) ya ce ‘ubanka’ ne, sai kawai na ji an yi harbi su ma sai suka mayar da martani ni kuma sai na ruga cikin gida a guje,” inji ta cikin kuka.

Wani mutum da shi ma ya ce masu garkuwar  sun shiga gidansa suna nemansa amma da iyalinsa suka fada musu baya nan sai suka shiga binciken dakin har suka dauke masa Naira dubu 450.

“Wannan ya sa muke kara yin kira ga gwamnatin Jihar Kaduna ta kara kokari domin kare rayukanmu, musamman a wannan yanki na Rigasa,” inji shi.

Kwamandan JTF, Aminu Sani wanda yana cikin wadanda suka kai dauki unguwar ya ce barayin sun kai 30. Ya ce sun yi kokarin kama wadansu daga cikin barayin amma hakan bai yiwu ba amma sun yi nasarar kubutar da wadansu mutane da barayin suka nemi sacewa a daren.

Mai unguwar yankin Malam Aminu Alhassan ya ce da ba don zuwan ’yan sanda da ’yan JTF a kan lokaci ba, Allah kadai Ya san yawan mutanen da za a kwashe a wannan dare.

Ya roki gwamnati ta kara tsaurara matakan tsaro musamman a yankin Rigasa.

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya ce zai yi magana da DPO na Rigasa kafin ya ce wani abu kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai kira wakilinmu ba.