Aminiya

An yi garkuwa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da yin garkuwa Kwamandan shiyyar Karamar Hukumar Suleja kuma Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa Rambo. An samu rahoton yin garkuwa da ACP Musa, ne lokacin had yake hanyarsa ta zuwa Jos babban birnin jihar Filato a jiya Asabar.

Masu garkuwan sun bukaci a biya kudin fansa Naira Miliiyan 50.

ADVERTISEMENT

Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta sanar da cewa, an samu motar ACP Musa ne a hanya kusa da gadar Kanock da ke tsakanin jihohin Kaduna da Nasarawa, a lokacin da jami’an ‘yan sandan ‘Operation Safe Haven’ ke aiki a yankin.

ADVERTISEMENT