Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An yi garkuwa da miji da mata a jihar Kogi

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi, Mista Hakeem Busari, a yau Litinin ya tabbatar da yin garkuwa da Mista Henshaw Ativie da matarsa a jiya Lahadi da wasu ‘yan bindiga suka yi.

Kwamishinan ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN hakan yau a Lokoja babban birnin jihar Kogi, inda ya ce an yi garkuwa da miji da matar ne a hanyar garin Itakpe zuwa Adogo da ke karamar hukumar Adavi a jihar.

ADVERTISEMENT

Mista Hakeem, ya ce an yi garkuwa da ma’auratan da daya daga cikin dan su mai shekara 7 da kuma wasu tagwaye mata `yan shekara 4 lokacin da suke cikin motar su kirar Jeep da nufin zuwa jihar Edo suka hadu da masu garkuwan.

ADVERTISEMENT