Da Dumi Dumi

An yi garkuwa da mutum 49 a Katsina

Dagacin kauyen Wurma da ke Karamar Hukumar Kurfi na Jihar Katsina, Alhaji mustapha Muhammed ya bayyana yadda ’yan bindiga suka sace mutum 49 a kauyensa.

Da yake yi wa ’yan jarida bayani kan yadda lamarin ya faru, Mohammed cewa ya yi, “sun shiga kauyen da bindigogi, amma ba su kashe kowa ba. Sai sun kwashe mutum 49. Daga baya sun saki mutum 11, sannan kuma na samu labarin cewa mutum daya ya sake dawowa. Muna kira ga gwamnati da ta taimaka ta kara mana jami’an tsaro, ko ba komai kasancewarsu a kusa yana ba ’yan bindigar tsoro.

Wani mazaunin kauyen na Wurma, Badamasi Wurma wanda aka dauke matarsa da ’ya’yansa uku cewa ya yi, “muna tare da abokaina da misalin karfe 11 da rabi na dare sai muk ji harbin bindiga, shi ne sai muka fara gudu, ba mu sake haduwa ba sai washegari,” inji, inda ya da kara da cewa ’yan bindigar sun kai kimanin 300.

“Sun shiga gidana suka tafi da matata da ’ya’yana. Sannan suka kwashe abubuwan da za su iya kwasa suka tafi. Wasu daga cikin wadanda aka kwasa sun dawo, ciki har da diyata guda daya. Amma har yanzu matanmu da ’ya’yanmu suna wajensu.

…An kubutar da daliban Jami’ar ABU da ake sace

ADVERTISEMENT

A wani labarin kuma, an kubutar da daliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga hannuna masu garkuwa da mutane wadanda aka sace ranar Litinin da ta gabata da yamma.

Daliban su ne Fatima Jalingo da Maryam Bello da Umar Sagir wadanda suke ajin karshe a jami’ar.

Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce, “an saki daliban Jami’ar ABU wadanda suke cikin wadanda aka sace a ranar 26 ga watan Agusta, 2019 a hanyar Kaduna zuwa Abuja, kuma tuni suka koma gidajensu.

Idan ba a manta ba, a ranar Litinin da misalin karfe 6 da minti 50 na yamma ne aka samun labarin masu garkuwa da mutane sun tare hanya, inda suka bude wa motoci wuta, suka kashe mutum uku, suka yi garkuwa da mutum shida, kamar yadda sanarwar ’yan sanda jihar Kaduna ta nuna.

Share