Daily Trust Aminiya - An yi garkuwa da sama da mutum 100 a cikin wata 9 – Gwamnan
Subscribe

An yi garkuwa da sama da mutum 100 a cikin wata 9 – Gwamnan Taraba

Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku, a yau Alhamis ya ce an samu adadin sama da mutum 100 da aka yi garkuwa dasu daga watan Janairu zuwa Satumba 2019.

Gwamna Darius, ya sanar da hakan ne yau a Jaingo babban birnin jihar a wani taron horarwar kwana daya mai taken “Operation Ayem-Akpatuma II“ wanda rundunar sojojin Najeriya reshen Jos ta shirya.

Gwamnan ya kara da cewa, a watan Satumba kadai an samu adadin mutum 30 da aka yi garkuwa da su a jihar, wanda hakan ya yi sanadiyyar asarar kudi daga Naira miliyan 200 zuwa miliyan 250 don kubutar da wadanda aka yi garkuwan da su a matsayin kudin fansa.

texem
More Stories