✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da sarkin Adara

A jiya Jumu’a ce wasu da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da babban sarkin Adara Mai Alfarma Maiwada Galadima III.…

A jiya Jumu’a ce wasu da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da babban sarkin Adara Mai Alfarma Maiwada Galadima III.

An yi garkuwa da shi ne tare da matarsa a lokacin da suke tafiya daga cikin garin Kaduna zuwa fadarsa da ke cikin Kachia a Kudancin Kaduna.

Har yanzu babu labarin dogaransa, amma dai an samu rahoton cewa an ga direbansa duk da cewa ba ya cikin hayyacinsa.