✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da Darakta tare da kashe danta a Kaduna

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wata Darakta a Kotun Shari’ah ‎mai suna Hajiya Aishatu Muhammad Munjalo a…

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wata Darakta a Kotun Shari’ah ‎mai suna Hajiya Aishatu Muhammad Munjalo a gidanta da ke Doka Mai Jama’a yankin Kujama a Karamar Hukumar Chikun a jihar Kaduna.

‎Masu garkuwan sun kuma harbe danta mai Suna Abdurrauf Muhammad bayan ya yi kokarin hana su tafiya da mahaifiyarsa.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 6:30 na safiya jiya Laraba a lokacin da suka yi wa gidan dirar mikiya.

Aminiya ta samu bayanin cewa, tuni aka yi wa mamacin sutura a yayin da kuma yan uwan ke jiran masu garkuwa da mutane su kira domin sanin halinda Hajiyar ke ciki.

‎Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ‎ DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce, tuni sun tuntubi sashen da yake da masu garkuwa da mutane domin su taimaka wajen gano mutane.