✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkwa da tsohon Kakakin PDP na Katsina

’Yan bindiga sun yi garkuwa da da tsohon Shugaban Matasa kuma tsohon Kakakin Jam’iyyar PDP a Jihar Katsina, Alhaji Salisu Ali Sukuntuni. Majiyarmu ta ce…

’Yan bindiga sun yi garkuwa da da tsohon Shugaban Matasa kuma tsohon Kakakin Jam’iyyar PDP a Jihar Katsina, Alhaji Salisu Ali Sukuntuni.

Majiyarmu ta ce da misalin karfe ukun daren Alhamis ne mharan suka shiga garin na Sukuntuni da ke Karamar Hukumar Kankiya, suka yi awon gaba da shi daga gidansa.

Majiyarmu ta ce Alhaji Salisu Sukuntuni ya je garin ne domin halartar ta’aziyar mahaifinshi kuma zuwa lokacin rubuta wannan rahoton babu wani bayani daga iyalansa ko wata kafar ta daban dangane da halin da yake ciki.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar hakan.

An sace shi ne kwana biyu bayan masu garkuwa da mutane sun dauke kanwar Shugaban Bankin Bayar da Rance Gina Gidaje, Alhaji Ahmad Musa Dangiwa wadda har yanzu babu wani labari a kanta.

An dai dauke ta ne da misalin karfe daya na dare a unguwar Sabuwar Abuja da ke cikin garin Kankiya.