Da Dumi Dumi

An yi jana’izar Magaji Ubandoman Gombe

An yi wa Alhaji Magaji Muazu (Ubandoman Gombe) sallar jana’iza a fadar sarkin Gombe, an kuma birne a makabartar da ke hanyar Bajoga a jihar Gombe.

An yi wa marigayin sallar jana’iza da misalin karfe 4:45 na yamma, limamin babban masallacin jihar Gombe Sheikh Muhammad Pindiga ne jagoranci sallar, sarakuna da ma’aikatan gwamnati da dama ne suka halarci sallar, cikin su akwai mataimakin gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Audu Sule Katagum, da sauran manyan ma’aikatan gwamnati.

 

Share